Hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta NDLEA tace ta kame wasu mutane
dake kokarin safarar kwayoyi da tabar wiwi ga wasu ‘yan kungiyar Boko
Haram dake a wasu kauyuka a jihar Borno.
Hukumar ta bayyana hakanne a lokacin da ta gurfanar da wasu mutane
guda biyar da ake zarginsu da safarar kwayoyin. An dai kame mutane Uku a
tashar motar Muna, inda sukayi kokarin daura kwayoyin mota domin
safararsu. Su kuma sauran mutanen Biyu an kame su a karamar hukumar Biu
dake kudancin jihar Borno.
Mr Ona Ogilegwu, wanda shike zaman kwamandar hukumar yaki da fataucin
miyagun kwayoyi, shine ya sanar da hakan ga manema labaru lokacin da ya
gurfanar da mutanen, ya kuma ce suna ci gaba da saka ido don ganin suna
samun nasara ga ire iren mutanen da suke da tabbacin cewa sune ke kaiwa
‘yan kungiyar Boko Haram kwayoyi.
Da yake yiwa wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda karin haske, daya
daga jami’an hukumar Garba Mohammed Bala, yace anyi niyyar daukar kayan
ne zuwa Gamboru, kuma an kama tabar wiwi har da wasu kwayoyi har kilo
288.
Kasancewar hukumomi na kokarin ganin an sami zaman lafiya da
kwanciyar hankali a yankin sai gashi wasu mutane na kokarin daukar
kwayoyi suna kaiwa ‘yan Boko Haram.
A cewar Barista Kaka Shehu Lawan, kwamishinan ma’aikatar Shari’a
wanda kuma ya kasance shugaban kwamitin yaki da sha da fataucin miyagun
kwayoyi da gwamnatin jihar Borno ta kafa, yace da zarar an gama yaki da
Boko Haram, za a koma kan yaki da kwaya, kasancewar abin da ya hada da
kan ‘yan mata zuwa matan aure dayawa daga cikinsu na amfani da kwaya. VOA
No comments:
Post a Comment