Tuesday, 25 October 2016

Za'a Fara Rusau a Calais

Nan gaba kadan ne ake sa ran za a fara aikin rushe sansanin 'yan cirani da ke garin Calais a arewacin kasar Faransa wanda aka fi sani da Jungle.
A jiya litinin ne aka kwashe kusan kashi daya cikin 'yan cirani 8000 da ke zaune a sansanin, inda aka rarraba su wurare daban-daban a kasar Faransar.
Wakilin BBC ya ce ana saran za a sake kwashe wasu a yau talata, kuma za a fara aikin rusau din a yau talata, wannan dai alama ce da ke nuna an dauki koken da mutanen Calais suka yi na zaman yan ciranin a wurin da matukar muhimmanci.
Ya yin da ga hukumomi suka ce za a sanya ido sosai a dan tsakanin nan, dan gujewa sake zaman wasu sabbin 'yan ciranin a wurin, wanda hakan na nufin daukar matakan tsaro baya ga matakin rushe shi. BBC

No comments:

Post a Comment